🛡️🌿 YADDA AKE NEMAN KARIYA DA KUMA RUFEWAR KURWA DA RUHU DAGA SHARRIN MATS AFA DA MAYU 🌿🛡️
Hanyar hada maganin gargajiya ta amfani da Lalle,da karatun Al-Qur’ani
🌿 ABUBUWAN DA ZA A SAMO
🔹 Garin Lalle ko ganyensa: rabin tiya (½) ko tiya 1.
🔹 Ɗauri: kamar 30 (tsawon sau 30).
🧴 HANYAR HAƊAWA DA AMFANI
🚿 1. YIN WANKA
Bayan sallama sallar La’asar, a zuba garin Lallen a cikin ruwa (kamar robar fentin ƙarama), sannan a zuba ɗaure guda 1 a ciki, ko a riƙe shi cikin hannu ɗaya.
📖 2. KARATUN SURATUL MULK
A karanta Suratul Mulk ƙafa 10, tun daga farko har ƙarshe, a kan ruwan.
Bayan haka, a yi wanka da wannan ruwan.
Gobe ma haka za a sake yi, jibi ma haka, har tsawon kwana 3.
🌿 AMFANI DA SAURAN ƊAURE 27
Sauran ɗauren guda 27 ɗin da suka rage, za a riƙa tafasa su ana yin surace.
Idan ya huce, sai a riƙa shafawa ko yin wanka da shi har tsawon kwana 27.
🛡️ AMFANINSA DA TASIRINSA
Insha Allah, tare da dogaro ga Allah, ana yin wannan a matsayin wata hanya ta neman kariya da rufin kurwa da ruhi daga matsafa da mayu,da Shaiɗanun aljanu da ake aiki dasu wajen tsafe tsafe domin kada su samu nasarar cutarwa agareka.
🌿 Wannan hanyar tana da babbar fa’ida da dukkan masu amfani da ita ga wanda ke fama da:
🔹 Gane-gane
🔹 Muggan mafarkai
🔹 Tsoro da firgici
🔹 Ko mutumin da yake ganin kamar mayu sun kama shi ko sun tura masa aljannu domin ba shi tsoro.
🤲 Allah ne Mai Kariya kuma Mai iko a kan komai.
Wannan bayani yana bayyana amfani na gargajiya da na addini; bai kamata a ɗauke shi a matsayin madadin neman taimakon ƙwararren ma’aikacin lafiya ko malamin addini ba idan matsalar ta kasance mai tsanani.

No comments:
Post a Comment